Turkiya tayi alkawarin fitar da Sojojin ta daga cikin kasar Iraki
(last modified Thu, 22 Dec 2016 18:15:46 GMT )
Dec 22, 2016 18:15 UTC
  • Turkiya tayi alkawarin fitar da Sojojin ta daga cikin kasar Iraki

jakadar kasar Turkiya a birnin Bagdaza na kasar Iraki ya yi alkawrin fitar da Sojojin su daga cikin kasar

Kafar watsa labaran kasar Iraki ta nakalto Faruk Kimakcy jakadan kasar Turkiya a birnin Bagdaza yayin ganarwarsa da Nuri Maliki mataimakin Shugaban kasar Iraki a wannan Alkhamis na cewa kasar tana mutunta hukumar Iraki  da kuma dukkanin kasar ta, kuma nan ba da jimawa ba za su fitar da dukkanin sojojin su dake cikin kasar ta Iraki.

A nasa bangare Nuri maliki mataimakin Shugaban kasar ta Iraki ya tabbatar da fadada alaka tsakanin buranan Bagadaza da Ankara tare kuma da tuntubar juna wajen fahimtar juna kan abinda ya shafi kasashen biyu, har ila yau magabatan sun tattaunawa kan batutuwan da suka shafi tsaron Iraki da kuma yankin.

Wannan dai ba shi ba ne karo na farko da Gwamnati tare da mahukuntan kasar Irakin ke neman Gwamnatin Turkiya ta fitar da Sojojin ta daga kasar ta Iraki, to saidai Gwamnatin Turkiyar ta yi kunnan shegu a kan fakewa da yaki da ta'addanci.

A karshen shekarar 2015, Kasar ta Turkiya ta tura daruruwan Sojojin ta zuwa sansanin Ba'ashika na garin Mausil babban garin jihar Nainuwa ba tare da izinin Gwamnatin Iraki ba, bisa da'awar bayar da horo ga Dakarun Kurdawa na kasar dangane da yadda za su kalubalanci 'yan ta'adda.