Turkiya: Sojojin Turkiya Sun yi alkawalin Ficewa Daga Kasar Iraki
Jakadan Turkiya A Iraki ya ce sojojin kasarsa za su fice daga cikin kasar Iraki
Jakadan Turkiya A Iraki ya ce sojojin kasarsa za su fice daga cikin kasar Iraki.
Majiyar labari ta Somariyya ta Iraki, ta ambato jakadan kasar Turkiya a cikin Iraki Faruq Qimaqchi wanda ya gana da tsohon pira ministan kasar Nuril Maliki yana cewa; Gwamnatinsa tana girmama hurumin dukkanin iyakokin kasar Iraki kuma ba da jimawa ba za ta janye dukkanin sojojinta da su ke a cikin kasar ta Iraki ba.
A nashi, gefen Nuril Maliki ya jaddada wajabcin bunkasa alaka a tsakanin Bagadaza da Ankara da kuma yin aiki tare domin warware matsalolin yankin.
Gwamnatin kasar Iraki dai ta shi yin kira ga Turkiya da ta janye sojojinta da ta tura cikin kasar da sunan fada da ta'addanci.
A 2015 ne Turkiyan ta girke daruruwan sojojinta a sansanin Ba'ashiqah da ke gundumar Mosel da sunan za ta baiwa mayakan kurdawa na Pishmarga horon fada da ayyukan ta'addanci.