Firayi Ministan Iraki Ya Bukaci Erdogan Da Ya Girmama Hurumin Kasarsa
(last modified Sat, 31 Dec 2016 05:50:21 GMT )
Dec 31, 2016 05:50 UTC
  • Firayi Ministan Iraki Ya Bukaci Erdogan Da Ya Girmama Hurumin Kasarsa

Firayi ministan kasar Iraki Haider al-Abadi ya kirayi shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdogan da ya girmama hurumin kasar Irakin da kuma kokari wajen kyautata alaka ta makwabtaka da 'yan'uwantaka tsakanin kasashen biyun.

A wata sanarwa da fadar firayi ministan Abadin ta  fitar ta ce Haider al-Abadin ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da ta hada shi da shugaban Turkiyyan lamarin da  ake ganinsa a matsayin a wani babban mataki na kokarin magance matsalar da ta kunno kai tsakanin kasashen biyu sakamakon ci gaba da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Irakin da shugaba Erdogan din yake yi.

Sanarwar ta kara da cewa yayin tattaunawar dai firayi ministan na Iraki ya bayyana fatan cewa shugaba Erdogan din zai dau matakan da suka dace wajen kyautata alakar da ke tsakanin kasashen biyu wacce ta yi tsami ainun cikin 'yan shekarun baya-bayan nan.

Shi ma a nasa bangaren shugaban na Turkiyya ya taya firayin ministan na Iraki murnar nasarorin da dakarun kasar suke samu a kan ta'addan kungiyar Da'esh a kokarin da ake yi na kwato garin Mosul.