'Yan Kasar Yemen Miliyan 17 Ne Ke Fuskantar Barazanar Yunwa.
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i19738-'yan_kasar_yemen_miliyan_17_ne_ke_fuskantar_barazanar_yunwa.
Hukumar Samar da abinci ta MDD ta sanar da cewa kasar Yemen na bukatar taimakon gaggauwa na tsabar kudi Dala biliyan daya da miliyan 200 domin magance matsalar abinci musaman ma a wuraren da aka fuskanci fari inda kimanin 'yan kasar miliyan 17 ke fuskantar barazanar yunwa.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Apr 23, 2017 13:33 UTC
  • 'Yan Kasar Yemen Miliyan 17 Ne Ke Fuskantar Barazanar Yunwa.

Hukumar Samar da abinci ta MDD ta sanar da cewa kasar Yemen na bukatar taimakon gaggauwa na tsabar kudi Dala biliyan daya da miliyan 200 domin magance matsalar abinci musaman ma a wuraren da aka fuskanci fari inda kimanin 'yan kasar miliyan 17 ke fuskantar barazanar yunwa.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Mista Steven Anderson babban daraktan hukumar samar da abinci ta MDD a kasar Yemen, ya nuna kyakkyawan fatan sa na tattara taimakon gaggawa domin tallafawa Al'ummar kasar Yemen da matsalar yaki da fari ya daidaita.

Mista Steven Anderson ya kara da cewa matukar dai ba a hada wannan taimakon ba to ba shakka Al'ummar kasar Yemen din za su kara shiga cikin mayuwacin hali, sannan kuma ya ce za a gudanar da taron taimakon kafafen yada labarai ga kasar Yemen a birnin Geneva domin sanar da sakamakon bincike na Hukumar samar da abinci musaman kan matsalar rashin abinci a kasar ta Yemen.

A ranar Talata 25 ga wannan wata na Avrilu dake muke ciki ne ake sa ran za a gudanar da wannan taro mai mahimanci a birnin Geneva domin fadakar da Duniya kan halin kunci da rashin abinci da Al'ummar kasar Yemen ke ciki.