Alhuthi: Amurka Da Isra'ila Ne Tushen Matsalolin Gabas Ta Tsakiya
(last modified Mon, 24 Apr 2017 07:01:20 GMT )
Apr 24, 2017 07:01 UTC
  • Alhuthi: Amurka Da Isra'ila Ne Tushen Matsalolin Gabas Ta Tsakiya

Jagoran kungiyar Ansarullah a kasar Yemen ya bayyana Amurka da Isra'ila a matsayin ummul haba'isin dukkanin matsalolin yankin gabas ta tsakiya.

Tashar talabijin ta Almasira daga kasar Yemen ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a daren jiya wanda kafofin yada labaran kasar Yemen suka watsa kai tsaye, jagoran kungiyar Ansarullah Sayyid Abdulmalik Alhuthi ya bayyana cewa, Amurka da Isra'ila su ne ke hannu a dukkanin matsalolin yankin gabas ta tsakiya.

Ya ce Amurka da Isra'ila ne suke yaki da al'ummar kasar Yemen, inda ya ce Saudiyyah tana a matsayin kayan aiki ne  kawai a hannunsu, kuma wannan ita ce siyasar Amurka da Isra'ila a kan kasashen larabawa da na musulmi da ma sauran kasashe masu 'yancin siyasa, duk al'ummar da ta ce za ta rayu cikin 'yanci Amurka da Isra'ila za su yake ta, ko dai kai tsaye, ko kuma ta hanyar yin amfani da 'yan korensu, kamar yadda a halin yanzu suke yaki da Yemen ta hanyar yin amfani da Saudiyya.

Ya kara da cewa ana zargin al'ummar Yemen da suka ki bayar da kai bori ya hau da cewa su yaran Iran ne, saboda sun zabi su rayu cikin 'yanci, da kin mika wuya wuya ga munufofin siyasar Amurka da Isra'ila da kuma karnukan farautarsu a yankin gabas ta tsakiya.