Damuwarr WHO Kan Halin Da Ake Ciki A Yemen
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce halin da ake ciki a kasar Yemen ya wuce duk tunanin da ake, duba da yadda lamuran agaji ke kara dagulewa.
Kimanin mutane miliyan 19 ne ke bukatar agaji a wannan kasa ta Yemen dake fama da yaki yau sama da shekaru biyu.
Hukumar ta ce tun kafin dama abubuwa su kara dagulewa a Yemen, da akwai matsaloli da dama da kasar ke fama dasu wadanda suka hada da rikicin siyasa da talauci.
Hukumar ta WHO ta ce tun bayan tsanantar rikici a kasar ta Yemen an kai hare-hare 325 kan cibiyoyin kiwan lafiya, makarantu, kasuwanni hanyoyi da mayan gine-gine wanda hakan ya hadassa tsarin matsaloli da suka kai ga jefa al'umma cikin halin kaka-ni-kayi.
Hukumar ta lafiya ta ce duk da cewa an samu sauki bayan daukan kwararen matakai bayan barkewar cutar Kwalera a 2016 inda mutane 24,000 suka kamu, a yanzu abun da yafi daukan hankali shi ne karin bukatuwar agajin jama'a akan sha'anin kiwan lafiya.
A cewar hukumar ta WHO cututuka irinsu ciwan sukari, hawan jini da cutar daji a yanzu sun fi barin wutar da ake kisa.
Tun dai faruwar rikicin a wannan kasa ta Yemen a watan Maris na 2015, safara magunguna na daukan yaunin maras alafiya zuwa cikin kasar ya fuskanci koma baya da kashi 70%, ko dai ya kasance magungunan sunyi kadan ko kuma babu su ma kwata-kwata.
Ko bayan ga hakan a cewar hukumar tabarbarewar al'amuran gudanarwa a asibitoti shi ma na taka tasa muhimiyar rawa, kimanin asibitoci 300 aka kai ma hari ko aka lalata, baya ga rashin biyan albashi na ma'aikatan lafiya.
Kana kuma babban abun damuwa shi ne yunwa dake adabar kusan illahirin al'ummar kasar lamarin daya jefa yara da mata masu juna biyu cikin tamowa.
A game da dukkanin wadanan matsalolin hukumar ta ce tana son cimma guri guda uku hadin gwiwa da abokan hulda.
Na farko dai shi ne kara karfafawa da kuma fadada shirin shawshawa da kuma sa 'ido kan cututukan dake zama annoba, inda ko a watan da ya gabata yara kimanin miliyan biyar ne akayiwa allura riga kafin cututukan kyanda ko dusa da kuma shan inna ko Polio, wanda ta ce a wannan shirin kawai an yi amfani da motocin haya sama da 5,000 wanda ta ce misali ne kada daga cikin bukatun da ake da wajen kawo agaji a sha'anin kiwan lafiya a inda ake fama da rikici.
Na biyu shi ne samar da sha'anin kula da kiwan lafiyar al'umma a matakin farko cikin kananan asibitoci, sanan na uku kuma shi ne kula da masu fama da cututuka irin na yau da kulun
A wtan fabrairu na 2017 tonne takwais na maguguna da kayan aiki na bukata ne hukumar ta samu isar da su a yankin Taiz na kasar ta Yemen, wanda kuma ya shafi mutane 350,000 dake cikin sananin bukata.