Yemen / HWO : An Samu Raguwar Kisa Na Cutar Kwalera
Jun 27, 2017 11:03 UTC
Hukumar lafiya ta duniya ta ce an samu raguwar kisa na cutar amai da gudawa a Kasar Yemen, wacce ta yi sadadin mutuwar mutane 1,400 a cikin wata biyu a wannan kasa.
Cutar kwalera ta samu yaduwa cikin sauri a wannan kasar ne sakamakon luguden wuta na ba dare ba rana da kawacen da Saudiya ke jagoranta ke kaiwa wanda kumake shafar cibiyoyin lafiya da asibitoci.
Adadin wadanda suka kamu da cutar ya ragu daga 41,000 zuwa 39,000 a cewar mashawarcin hukumar ta WHO mai kula da harkokin agajin gaggawa a Yemen, Ahmed Zouiten.
Yemen dai ita ce kasa mafi talauci a kasashen yankin larabawa na tekun fasha.
Tags