Qatar Ta Bukaci Diyya Ga Abokan Gabarta
(last modified Mon, 10 Jul 2017 06:18:20 GMT )
Jul 10, 2017 06:18 UTC
  • Qatar Ta Bukaci Diyya Ga Abokan Gabarta

Kasar Qatar ta sanar da kafa wani kwamiti da zai bukaci kasashen larabawa abokan gabarta da su biya ta diyya bayan maida ta saniyar ware na tsawan makwanni biyar a yanzu.

Kwamitin dai zai maida hankali kan yadda za'a biya diyya ga wasu mayan kamfanoni na kasar da suka hada da Qatar Airways da wasu dalibai da aka koro daga kasashen larabawan inda suke da rejista.

Babban mai shigar da kara na gwamnatin kasar ta Qatar, Ali ben Fetais al-Marri, ya bayyana a wani taron manema labarai a birnin Doha cewa kwamitin zai saurari kararaki daga wasu bangarori da wasu daidaikun mutane.

Akwai yiwuwar kuma kwamitin zai gabatar da kararrakin da suka shafi kamfanin jirgin sama na kasar da wasu bankuna har zuwa gaban kotunan ketare ciki har da Paris da Landan.

Yankin Golfe dai ya fada cikin rikicin diflomatsiya  mai tsanani tun lokacin da makobtan na Qatar da suka hada Saudiyya, Hadaddiyar daular Larabawa da Bahrain, da kuma Masar a daya bangare suka sanar da katse duk wata irin hulda da  Qatar din bisa zarginta da taimakawa ayyukan ta'addanci, batun da mahukuntan na Qatar suka jima suna musuntawa.