Hadaddiyar Daular Larabawa Ta Ja Kunnen Kasar Katar
(last modified Wed, 19 Jul 2017 11:10:20 GMT )
Jul 19, 2017 11:10 UTC
  • Hadaddiyar Daular Larabawa Ta Ja Kunnen Kasar Katar

Jakadiyar kasar ta Hadaddiyar Daular Larabawa A MDD ta ce idan har kasar ta Katar din ba ta karbi sabbin sharuddan da aka kafa ma ta ba to za a korarta daga kungiyar larabawan yankin tekun pasha.

Jakadiyar kasar ta Hadaddiyar Daular Larabawa a MDD ya ce idan har kasar ta Katar din ba ta karbi sabbin sharuddan da  aka kafa ma ta ba, to za a korarta daga kungiyar larabawan yankin tekun pasha.

Kamfanin dillancin labarun Associated Press ta bada labarin cewa; Jakadiyar  Hadaddiyar Daular ta Larabawa a Majalisar Dinkin Duniya Lana Nusaibah, ta ce;  Kasashen da su ka kakabawa Katar takunkumi suna son ganin kasar ta Katar ta yi aiki da bangare na shida na sharuddan wanda ya shafi fada da ta'addanci.

Shi ma wakilin kasar Saudiyya a Majalisar Dinkin Duniya Abdullahi al-Mu'allimi kasashen hudu da su ka kakabawa Katar takunkumi sun sake jaddada wajabcin ganin kasar ta yi aiki da sharadin fada da ta'addanci.