Afganistan : An Tsaurara Matakan Tsaro A Yayin Bikin Kasa
(last modified Sat, 19 Aug 2017 11:08:29 GMT )
Aug 19, 2017 11:08 UTC
  • Afganistan : An Tsaurara Matakan Tsaro A Yayin Bikin Kasa

A Afganistan an tsaurara matakan tsrao a yayin da ake cikin gudanar bukukuwan zagayowar ranar samun yancin kai a yau Asabar.

Bayanai daga kasar sun ce jami'an tsaro na cikin shirin ko ta kwana a a wannan kasa data jima tana fuskantar hare hare.

'Yan sanda a kasar dai sun tsaurar kwararen matakai na tsaro a Kabul babban birnin kasar domin kaucewa hare-haren 'yan Taliban, an kuma kafa shingayen binkice a galibin biranen kasar da kuma ofisoshin jakadanci na kasashen waje dake a kasar.

A ranar 19 ga watan Agusta na 1919 ne bisa yarjejeniyar Rawalpindi kasar Birtaniya ta amunce da baiwa Afganistan 'yancin kai, bayan yakin Ingila da Afganistan na uku duk da cewa kasar ba ta taba kasancewa mamba ba a daular ta Birtaniya.