Kasar Katar Ta Kai Karar Saudiyya A gaban Majalisar Dinkin Duniya
(last modified Sun, 20 Aug 2017 18:13:59 GMT )
Aug 20, 2017 18:13 UTC
  • Kasar Katar Ta Kai Karar Saudiyya A gaban Majalisar Dinkin Duniya

Karar da Kasar ta Katar din ta shigar ta shafi barazanar da Saudiyyar ta yi na harbo jiragen fasinjanta.

Kamfanin dillancin labarun Xinhua ya  ambato wani rahoto na kafafen watsa labarun Saudiyya da aciki suka bai wa Saudiyyar da sauran kasashen da suke rikici da Katar din hakkin barho jiragen fasinjanta matukar suka karaci sararin samaniyarsu.

Rahotnnin sun zargi Katar da kokarin amfani da jiragen samanta domin haddasa razana da firgita.

Kasashen Saudiyya, Bahrain, Masar, da Hadaddiyar Daular Larabawa, sun yanke alakar diplomasiyya da katar,saboda zarginta da taimakawa ta'addanci.