Kungiyar Ansarullah Ta Tabbatar Da Kalubalantar Sojojin Hayar Saudiya
Wani Jigo a majalisar siyasar kungiyar gwagwarmayar ansarullah ta kasar yemen ya tabbatar da cewa za su tsananta kalubalantar duk wani hari wuce gona da iri na sojojin hayar saudiya
Salim Almaglas ya bayyana haka ne a wannan assabar inda ya ce kasar yemen za ta shiga wata sabuwar gwagwarmaya na kalubalantar masu fice gona da iri na kasashen larabawa karkashin masarautar saudiya, inda za a kara yawan dakarun dake yaki da sojojin hayar saudiya a yankuna daban daban na kasar.
Almaglas ya bayyana cewa ta'addanci da kawancen saudiya ke yi kan al'ummar kasar yemen, ya kara hada kan al'ummar kasar tare da kara azama wajen kalubalantar kawancen masarautar saudiya.
A jiya juma'a ma jirgen yakin kawancen saudiyar sun yi lugudar wuta kan gidajen fararen hula na anguwar Atan dake birnin sana'a fadar milkin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwa da kuma jikkatar mutane 12.