Taron Ministocin Harkokin Waje Na Kungiyar Kasashen Larabawa A Al-Kahira
(last modified Tue, 12 Sep 2017 18:56:43 GMT )
Sep 12, 2017 18:56 UTC
  • Taron Ministocin Harkokin Waje Na Kungiyar Kasashen Larabawa A Al-Kahira

Ministocin harkokin waje na kasashen kungiyar kasashen Larabwa sun gudanar da taro na yini daya a yau Talata a birnin Al-kahira na kasar Masar, inda suka tattauna sauye sauyen da aka samu a yankin a cikin yan watannin da suka gabata .

Majiyar muryar JMI daga birnin Alkahiri ta nakalto babban sakataren kungiyar Ahmad Abul-gaida yana fadar cewa dole ne a gaggauta isar da agjagi ga yankunan da aka kubutar daga hannun yan ta'adda a kasashen Iraqi da siria, sannan a tallafa don ganin rayuwa ta koma kamar yadda take.

Majiyar ta kara da cewa ministocin sun tattauna dangane da halin da ake ciki a kasashen Yemen da Iraqi da kuma yadda zasu tallafawa shirin yaki da ayyukan ta'addanci a yankin. 

Pierre Krasnbal Jami'i hukumar bada agajin gaggawa ta MDD ya sami halattan taron na ministocin kungiyar kasashen Larabawa a yau, ya kuma bukaci taimakon kasashen don ganin hukumarsa ta sami damar isar da tallafin gaggawa ga  Palasdinawa wadanda suke rayuwa a sansanonin yan gudun hijira a kasashen yankin wadanda yawansu ya kai miliyon 5 da dubu 300.