Nov 04, 2017 12:03 UTC
  • Fiye Da 'Yan Hijira 700 Ne Suka Tsira Daga Halaka A Tekun Midtireniya

Kamfanin dillancin labarun Reuters ya ambato cewa; Masu Tsaron Ruwan Italiya Sun tseratar da mutanen ne a jiya jumaa.

Sai dai jami'an tsaron sun sanar da cewa sun tsamo gawawwakin mutane 23 tare da tseratar da wasu 64.

A bisa rahoton na Reuters, adadin wadanda aka tseratar da su daga nitsewa a jiya juma'ar sun kai 764.

Tekun  Medtireniya yana daga cikin yankunan da 'yan gudun hijira suke kokarin shiga cikin nahiyar turai.

A cikin wannan shekarar ta 2017 an kame mutane fiye da 18,000 da wasu 800 da suka so ketarawa cikin turai din.

Tags