Yemen : Adadin Masu Cutar Kwalera Ya Kai Milyan Guda
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i26571-yemen_adadin_masu_cutar_kwalera_ya_kai_milyan_guda
Kungiyar agaji ta kasa da kasa (Red Cross) ta ce adadin mutanen da ke fama da cutar amai da gudawa cewa da kwalera a Yemen ya kai miliyan guda.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Dec 21, 2017 11:00 UTC
  • Yemen : Adadin Masu Cutar Kwalera Ya Kai Milyan Guda

Kungiyar agaji ta kasa da kasa (Red Cross) ta ce adadin mutanen da ke fama da cutar amai da gudawa cewa da kwalera a Yemen ya kai miliyan guda.

Kungiyar wacce ta bayana hakan a shafinta na Twitter ta ce hakan wata alama ce ta nuna yadda kasar ke kara fadawa cikin mayuyacin hali.

Yau sama da shekara biyu kenan da kawacen da Saudiyya ke jagoranta ke kai farmaki kan kasar ta Yemen, lamarin da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane da kuma cilastawa wasu milyoyin yin gudun hijira.