Gwamnatin Kasar Tunisia Tana Goyon Bayan Al-ummar Palasdinu
Ministan harkokin wajen kasar Tunisia ya bayyana cewa gwamnatin kasarsa ba za ta taba rabuwa da al-ummar Palasdinu ba.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Khamis Al-Jahinawi yana cewa amincewa, da kudurin babban zauren MDD wanda mafi yawan kasashen duniya suka yi wata babban hujja ce ta cewa kasashen duniya basu yarda da matsayin shugaban kasar Amurka kan Qudus ba kuma suna goyon bayan al-ummar Palasdinu.
A ranar Alhamis da ta gabata ce, a wani zaben da MDD ta shirya kan matakin da Trump ya dauka kan Qudus, kasashen duniya 128 suka amince da kudurin mai goyon bayan Palasdinawa da kuma yin watsa da Amurka kan wannan lamarin, sai kuma wasu tsirarun kasashe wadanda basu fi 9 suka nuna goyon bayansu ga shugaban Amurakan, a yayinsa wasu kasashe 35 suki ki shiga zaben.
An kada wannan kuri'ar ce bayan da kasar Amurka, ita kadai a komitin tsaro na MDD mai membobi 15,ta goyon bayan shugaban kasarta kan wannan batun.