Yahudawa Sahyuniya Sun Rusa Gidan Palastinawa 132 A Qudus
Wata cibiyar kare hakin bil-adama a Palastinu ta sanar a wannan Talata cewa 'Yan Sahayuniya sun rusa gidajen Palastinawa 132 a birnin Qudus cikin shekarar 2017 da ta gabata.
Hukumar Radio da Talabijin ta kasar Iran ta nakalto cibiyar kare hakin bil-adama a birnin Qudus na cewa rusa wadannan gidaje ya jefa iyalai 240 cikin mawuyacin hali na rayuwa.
Sanarwar da cibiyar kare hakin bil-adama ta Palastinu ta fitar ta ce binciken da ta gudanar zuwa karshen ranar 31 ga watan Disamban shekarar 2017 da ta gabata ya tabbatar da cewa sama da hekta 900 ne na yankin Palastinu, Haramtacciyar kasar Isra'ila ta mamaye a gabar yammacin Jodan da nufin gina gidajen yahudawa.
Sanarwar ta kara da cewa gine-ginen gidajen yahudawa a yankunan Palastinawa ya karu da kashi 30% a shekarar 2017 idan aka kwatamta da wadanda aka yi a shekarar 2016, dukkanin wadannan gine-ginen da yahudawan ke yi ya sabawa dokokin kasa da kasa.