Abu Gaiz:Akwai Wuya A Magance Rukicin Kasar Yemen
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i29846-abu_gaiz_akwai_wuya_a_magance_rukicin_kasar_yemen
Babban saktaren kungiyar kasashen Larabawa ya bayyana cewa akwai wuya a magance rikicin kasar Yemen
(last modified 2018-08-22T07:01:41+00:00 )
Apr 12, 2018 06:45 UTC
  • Abu Gaiz:Akwai Wuya A Magance Rukicin Kasar Yemen

Babban saktaren kungiyar kasashen Larabawa ya bayyana cewa akwai wuya a magance rikicin kasar Yemen

Cikin wata tattaunawa da ya yi da jaridar Alhayat, babban saktaren kungiyar kasashen Larabawa ya ce a halin da ake yanzu akwai wuya a iya magance rikicin kasar yemen ta hanyar siyasa.

Abu Gaiz ya ce, a ranar lahadi mai zuwa, za su gudanar da zama da birnin Dammam na kasar Saudiya, kuma za su mayar da martani kan kasar Iran saboda tana baiwa kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen makamai suna harbwa kasar Saudiya.

Har ila yau Abu Gaiz ya kara da cewa a wannan taro za su dauki mataki kan kisan gillar da hukumomin haramtacciyar kasar Isra'ila ke yi kan al'ummar yankin zirin gaza.