An Yi Gargadin Sake Billar Cutar Kwalara A Yemen
Masu bincike da likitocin kasa da kasa sun yi gargadin sake billar cutar kwalara cikin kashi 54% na yankunan kasar yemen da hakan na iya yin sanadin kamuwar milyoyin mutanan kasar
Tashar Talabijin din Al-alam dake watsa shirye-shiryenta daga nan birnin tehran ta ce har ila yau ya yi ishara da kamuwar mutane akalla miliyan 14 da cutar ta kwalara a kasar ta yemen, inda suka bukaci mahukuntan kasar da su dauki kwararen matakan gaggauwa da suka hada da samar da tsabtaceccen ruwan sha, gyara magudanar ruwa da kuma gudanar da alurar riga kafi.
Har ila yau, Shugaban ofishin kungiyar kai agaji ta kasa da kasa a kasar ta Yemen Alexander Fit ya ce kimanin yamaniyawa dubu biyu ne suka rasa rayukansu cikin watani 6 da suka gabata, sanadiyar kamuwa da cutar kwalara.
A cewar Abdul-salam Madani, mataimakin ministan kiyon lafiyar kasar Yemen, cibiyoyin kiyon lafiya da wuraren shan magani 415 ne suka rugushe dake a matsayin kashi 70% na cibiyoyin kiyon lafiya, sanadiyar hare-haren wuce gona da irin da kawancen saudiya ke kaiwa cikin kasar