Sayyid Hassan Nasarallah: Zaben 'Yan Majalisa Babbar Nasara Ce Ga Kasa
(last modified Mon, 07 May 2018 18:58:24 GMT )
May 07, 2018 18:58 UTC
  • Sayyid Hassan Nasarallah: Zaben 'Yan Majalisa Babbar Nasara Ce Ga Kasa

Babban magatakardar Kungiyar Hizbullah ta Lebanon ya bayyana haka ne dazu da ya gabatar da jawabi bayan fara fitowar sakamakon zaben 'yan majalisar dokokin kasar.

Har ila yau Sayyid Nasarallah ya yi ishara da yadda mutane su ka fito sosai a yayin zaben, sannan ya kara da cewa: Parpagandar da aka rika yi gabanin zaben domin bata sunan gwagwarmaya bai yi tasiri ba.

Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya ci gaba da cewa; Kasantuwar wakilan gwagwarmaya a cikin majalisar dokoki zai taimaka wajen cimma alkawullan yakin neman zabe.

Wannan shi ne karo na farko a cikin shekaru 9 da aka yi zaben yan Majalisa a cikin Lebanon bayan da aka rika daga lokacin yinsa a baya.

Ana hasashen cewa; idan aka kammala sanar da sakamakon zaben 'yan gwagwarmaya da kawayensu za su sami abinda zai karaci kujeru 40. Kungiyar Hizbullah da Amal kadai sun sami abinda ya kai kujeru 26.