Saudiyya Tana Ci Gaba Da Kai Hare-hare Akan Yemen
A kalla mutane biyar ne su ka kwanta dama a ci gaba da kai wa Yemen hari da sojojin Saudiyya suke yi
Tashar talabijin din al-alam ta ba da labarin cewa sojojin na Saudiyya sun kai hari har sau uku a yankin Sa'adah da ke arewacin kasar.
Wani labarin ya kunshi cewa; Jiragen yakin na Saudiyya sun kai wasu hare-haren a yankunan allhali da kuma bait faqiha da suke a gundumar alhudaidah.
Sai dai majiyar sojoji da kuma dakarun sa-kai na Ansarullah sun mai da martani akan wce gona da iri na Saudiyya ta hanyar harba makami mai linzami samfurin zilzal na biyu da kuma Badar 1 akan cibiyar kamfanin man fetur ta Aramco.
Fiye da shekaru uku kenan da sojojin Saudiyya su ke kai wa kasar ta Yemen hari wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci rayukan mutane fiye da 13,000.