Aug 28, 2018 12:56 UTC
  • MDD: Kisan Fararen Hula Da Saudiyya Ke Yi A Yemen Ya Zama Laifukan Yaki

Kwamitin da ke kula da kare hakkokin kananan yara da ke karkashin majalisar dinkin dinkin duniya, ya fitar da wani rahoto kan kisan kiyashin da Saudiyya take yi wa kananan yara a Yemen da cewa, hakan yana a matsayin laifukan yaki.

Kwamitin ya ce dole ne a kafa wani kwamiti na kasa da kasa da zai gudanar da bincike kan kisan fararen hula da Saudiyya take a Yemen, tare da mika sakamakon ga kotun manyan laifuka ta duniya domin hukunta masu laifi a cikin lamarin.

Sakamakon hare-haren da jiragen yakin Saudiyya ke kaddamarwa kan al'ummar kasar Yemen da sunan yaki da mayakan kungiyar Alhuthi, ta kashe faraen hula fiye da 13, da suka hada da dubban mata da kananan yara.

 

Tags