Gwamnatin Sahayoniya Ta Yi Barazanar Kashe Shugaban Kasar Siriya
(last modified Mon, 17 Sep 2018 19:07:05 GMT )
Sep 17, 2018 19:07 UTC
  • Gwamnatin  Sahayoniya Ta Yi Barazanar Kashe Shugaban Kasar Siriya

Ma'aikatar Yakin Sahayoniya ta watsa wasu hotuna tare da da'awar cewa wurin rayuwar Bashar Al-Asad ne inda ta yi barazanar hallaka Shugaban kasar ta Siriya

A ci gaba da mumunar siyasar mahukuntan haramtacciyar kasar Isra'ila na kokarin mamaya, a wannn Litinin ma'aikatar yakin 'yan Sahayoniya ta watsa wasu hotuna dake kumshe da filin saukar jiragen birnin Damuscus da tankunan yaki na kasar, inda ta yi da'awar cewa  wurin rayuwar Bashar Al-Asad ne tare da barazanar hallaka shi.

Ma'aikatar yakin ta 'yan Sahayoniya ta ce ta samu wannan hotuna ta hanyar amfani da wata sabuwar na'urar leken asiri samfarin Ofek-11.

Wannan dai bashi ba ne karon farko da  mahukuntan 'yan sahayoniya suke barazanar hallaka shugaba Asad, ko da a yayin da sojojin Siriya suka samu gagarumar nasara kan 'yan ta'adda a yankunan kudancin kasar, 'yan sahayoyinyar sun yi irin wannan barazana.