Dakarun Italiya Sun Ceto Dubban Bakin Haure A Tekun Bahar Rum
Rahotanni daga kasar Italiya sun bayyana cewar masu tsaron gabar tekun kasar sun sanar da da ceto bakin haure da adadinsu ya kai mutane 6500 a tekun Bahar Rum a jiya Litinin a hanyarsu ta zuwa kasar.
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya jiyo masu tsaron gabar tekun na Italiya suna cewa a jiya Litinin sun sami nasarar ceto wasu bakin haure su dubu 6 da 500 wadanda suke nufin shiga kasar daga kasar Libiya sannan kuma suka sami matsaloli a tekun na Bahar rum.
Mafi yawa daga cikin wadannan 'yan bakin hauren dai suna fitowa daga kasashen Afirka a kokarinsu na zuwa kasashen Turai din don neman dukiya da rayuwar da ta fi wacce suke ciki lamarin da ke sanya su hawa kananan jiragen ruwa marasa inganci daga gabar ruwan kasar Libya lamarin da a lokuta da dama yake haifar musu da matsaloli na nutsewa cikin Tekun.
A bisa kididdigar da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta fitar a ranar Juma'ar da ta gabata ta bayyanar cewa cikin wannan shekarar kawai kimanin bakin haure dubu 105 da 342 suka isa kasar Italiyan daga kasar Libiya sannan kuma kimanin mutane dubu 2 da 726 ne suka rasa rayukansu tsawon wannan lokacin a kokarin da suke yi na isar gabar ruwan kasar Italiyan.