Nuna Rashin Amincewar Majalisar Afghanistan Da Siyasar Kasar Saudiyya
(last modified Fri, 21 Oct 2016 03:46:52 GMT )
Oct 21, 2016 03:46 UTC
  • Nuna Rashin Amincewar Majalisar Afghanistan Da Siyasar Kasar Saudiyya

A ci gaba da nuna rashin amincewa da irin goyon bayan da kasar Saudiyya take ba wa kungiyoyin 'yan ta'adda a duniya, 'yan majalisar kasar Afghanistan sun yi kakkausar suka ga irin taimakon da kasar Saudiyyan take ba wa kungiyoyin ta'addanci da neman tada zaune tsaye na kasar.

Rahotanni daga kasar Afghanistan din sun bayyana cewa 'yan majalisar dokokin kasar Afghanistan din, cikin wata sanarwa da tattaunawar da suka yi da manema labarai, sun bayyana tsananin damuwarsu dangane da miliyoyin dalolin da gwamnatin Saudiyyan take ba wa 'yan kungiyar Taliban don tabbatar da manufofin Saudiyyan a kasar ta Afghanistan.

'Yan majalisar dai sun bayyana cewar a kowace shekara gwamnatin Saudiyyan  tana ba wa kungiyar Taliban, wacce take halin yaki da gwamnatin kasar Afghanistan din, dala miliyan 300 a matsayin kudaden taimako.

A saboda haka ne daya daga cikin 'yan majalisar mai suna Jamal Fakuri Beheshti ya bayyana cewar sun bukaci gwamnatin kasar Afghanistan din da ta sake nazarin alakar kasar da kasar Saudiyya, don kuwa gwamnatin Saudiyyan a koda yaushe ba wai kawai a kasar Afghanistan ba, hatta a kasar Pakistan da sauran kasashen duniya, ta kasance mai taimako da kuma goyon bayan kungiyoyin 'yan  ta'adda.

Shi ma a nasa bangaren Gholam Husain Nasiri, shi ma daya daga cikin 'yan majalisar kasar Afghanistan din, ya bayyana cewar a kowace shekara Saudiyya tana ba wa kungiyar Taliban miliyoyin daloli don cimma manufofinta da suka hada da haifar da yakin kabilanci a kasashen Afghanistan da Pakistan.

Irin wannan nuna rashin amincewa da siyasar Saudiyyan dai ya biyo bayan wata sanarwa ce da ofishin shugaban bangaren gudanarwa na gwamnatin Afghanistan din Abdallah Abdallah ya sanar da cewa a ziyarar da ya kai Saudiyyan ya tattauna da wasu jami'an kasar dangane da batun hanyoyin tabbatar da sulhu da zaman lafiya a kasar.

Ko shakka babu karuwar nuna rashin amincewa da irin goyon bayan da Saudiyya take ba wa 'yan kungiyar Taliban a kasar Afghanistan wani lamari ne da ke kara tabbatar da irin damuwar da ake da ita dangane da yadda gwamnatin Saudiyya take tsoma baki cikin harkokin cikin gidajen kasashen yankin ciki kuwa har da kasar Afghanistan.

Irin goyon bayan da gwamnatin Saudiyya take ba wa kungiyoyin 'yan ta'adda irin su Da'esh da Al-Qa'ida a kasashen Siriya da Iraki da Yemen ya sanya da dama daga cikin 'yan siyasar kasar Afghanistan jin cewa lalle mahukuntan Saudiyyan suna aikata hakan ne don cimma bakar aniyarta a kasar da ta hada da rarraba kan al'umma da haifar da yakin basasa a kasashen musulmi.

A kwanakin baya ma dai jami'ai da al'ummomin lardin Nangehar na kasar Afghanistan din sun nuna rashin amincewarsu dangane da kokarin Saudiyya na gina wata jami'a ta Musulunci a lardin saboda tsananin damuwar da suke ciki na cewa ba abin da za a koyar a wannan jami'ar da ya wuce yada akidar Wahabiyanci wanda a halin yanzu ake ganin ta a matsayin ummul aba'isin din dukkanin tsaurin ra'ayi da ayyukan ta'addanci da ake sanya matasan kasashen musulmi ciki.

Da dama dai suna ganin cewa irin taimakon kudade da Saudiyyan take bayarwa kungiyoyi da wasu kasashe, a bangare guda kuma da irin yadda take yada akidar Wahabiyanci, a hakikanin gaskiya wani kokari ne na  gwamnatin Saudiyyan na biyan bukata da kuma kokari wajen share fagen cimma manufofin Amurka da Ingila na rarraba kan musulmi da haifar da rikici a tsakaninsu bugu da kari kan shafa wa koyarwar Musulunci na hakika kashin kaji.