Sojojin Labanon Sun Kama Daya Daga Cikin Manyan Kwamandojin ISIS
Sojojin kasar Labanon sun sanar da nasarar kama daya daga cikin manyan kwamandojin kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh tare da wasu dakarun kungiyar su 10 a garin Arsal da ke arewa maso gabashin kasar ta Labanon a kan iyakan kasar da kasar Siriya.
A wata sanarwa da rundunar sojan ta Labanon ta fitar a yau din nan Juma'a ta ce sojojin sun kaddama da wasu hare-hare a safiyar yau a yankin Wadi al-Araneb da ke kimanin kilomita 124 arewa maso gabashin birnin Beirut, babban birnin kasar Labanon inda bayan gagarumin gumurzu suka samu nasarar kama daya daga cikin manyan kwamandojin kungiyar 'yan Da'esh din mai suna Ahmad Youssef Ammoun bayan sun raunana shi.
Sanarwar sojin ta kara da cewa baya ga shi wannan kwamandan, har ila yau sojojin sun kama wasu 'yan ta'addan su 10 baya ga wani adadi mai yawa na makamai da suka hada da albarusai da bama-bamai da ababe masu fashewa.
Sojojin Labanon din sun jima suna neman Ammoun saboda zarginsa da suke yi da taimakawa wajen dasa bama-bamai a cikin motocin da ake kai hare-haren ta'addanci da su cikin kasar ta Labanon, haka nan kuma ana zarginsa da jagorantar wasu hare-haren da aka kai wa jami'an tsaron Labanon din.