Taron Ministocin Harkokin Wajen Iran, Rasha Da Turkiyya Kan Rikicin Siriya
(last modified Tue, 20 Dec 2016 18:21:07 GMT )
Dec 20, 2016 18:21 UTC
  • Taron Ministocin Harkokin Wajen Iran, Rasha Da Turkiyya Kan Rikicin Siriya

Ministan harkokin wajen kasar Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewar Iran, Rasha da Turkiyya sun fara aiwatar da wani shiri na samo hanya ta diplomasiyya wajen magance rikicin kasar Siriya.

Ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana hakan ne a taron da ya hada ministocin harkokin wajen kasashen uku a birnin Mosko, babban birnin kasar Rasha don tattaunawa kan rikicin kasar Siriyan da yadda za a magance rikicin; inda ya ce: Babu yadda za a yi a magance rikicin kasar Siriya ta hanyar amfani da karfin soji, hanya guda kawai ta magance rikicin ita ce hanya ta diplomasiyya da tattaunawa.

A karshen taron dai, ministocin harkokin wajen kasashen uku, Muhammad Jawad Zarif na Iran, Sergei Lavroy na Rasha da Mevlut na Turkiyya sun fitar da wata sanarwar bayan taro da ta kumshi batutuwa daban daban da suka hada da girmama hurumin kasar Siriya da 'yanci da kuma hadin kan kasar. Hakan nan kuma da wajibcin amfani da hanyoyi na diplomasiyya wajen magance rikicin Siriya, kamar yadda kuma suka yi maraba da kokarin da aka yi na barin fararen hula su bar garin Aleppo da kuma bude hanyar da masu dauke da makami da suke wajen ma za su fice daga garin.

Wannan taron dai ya zo ne sakamakon nasarar da sojojin Siriya suka samu na kwace garin Aleppo daga hannun 'yan ta'addan da suke samun goyon bayan wasu kasashen duniya.