Italiya Ta Sanar Da Sake Bude Offishin Jakadancinta A Libya
(last modified Tue, 10 Jan 2017 06:34:59 GMT )
Jan 10, 2017 06:34 UTC
  • Italiya Ta Sanar Da Sake Bude Offishin Jakadancinta A Libya

Kasar Italiya ta sanar da sake bude offishin jakadancinta a Libiya, bayan rufe offishin a shekara ta 2015 kamar sauren kasashen yamma saboda matsalar tsaro.

A wannan Talata ce ake sa ran jakadan kasar Italiya a Libya zai gabatar da wasikar bude offishin a Tripoli babban birnin kasar ta Libiya, kamar yadda ministan cikin gidan kasar Italiya Marco Minniti ya sanar a yayin wani taron manema labarai na haddin gwiwa da ministan harkokin waje na gwamnatin hadakar kasar ta Libiya.

Saidai Ministan cikin gida na kasar Italiya bai yi karin haske ba akan yadda za'a tabbatar da tsaro bayan sake bude offishin jakadancin ba.

Birnin Tripoli dai ya sha fama da hare-hare kan ofisoshin jakadanci da kuma jami'an diflpmatsiyya.

Offishin jakadancin Italiya na daga cikin na baya baya da suka rufe kofofinsu a cikin watan fabrairu na 2015 bayan da wata kungiyar mayaka mai Fajr Libya ta kwace Tripoli babban birnin kasar bayan wani kazamin fada.