Kungiyar Tsaro Ta NATO Ta Jaddada Goyon Bayanta Ga Kasar Libiya
(last modified Wed, 01 Feb 2017 17:33:25 GMT )
Feb 01, 2017 17:33 UTC
  • Kungiyar Tsaro Ta NATO Ta Jaddada Goyon Bayanta Ga Kasar Libiya

Kungiyar tsaro ta NATO ta yi furuci da cewa: Dole ne ta goyi bayan kasar Libiya tare da taimaka mata a fagen yaki da ta'addanci.

A ganawar da ta gudana tsakanin babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg da fira ministan gwamnatin hadin kan kasar Libiya Fayiz Assaraj a birnin Bruksel na kasar Belgium: Jens Stoltenberg ya bayyana shirin kungiyarsa na goyon bayan siyasar gwamnatin hadin kan kasar Libiya tare da taimaka mata a fagen kalubalantar matsalolin tsaro da take fuskanta.

A nashi bangaren Fayiz Assaraj ya bayyana jin dadinsa kan shirin kungiyar tsaro ta NATO na taimaka wa kasarsa tare da jaddada burin gwamnatinsa na ganin ta hada kan dukkanin rundunonin sojin kasar karkashin jagoranci guda. Kamar yadda ya jaddada bukatar samun hadin kai tsakanin gwamnatinsa da kungiyar tsaro ta NATO a fagen yaki da ta'addanci da dakile matsalar kwararar bakin haure zuwa kasashen yammacin Turai ta kan iyakokin Libiya.