Feb 02, 2017 06:37 UTC
  • Unicef: Halin Da Kananan Yara Su ke Ciki A Gabacin Ukraine Ya Munana.

Asusun Kananan Yara Na Majalisar Dinkin Duniya ( Unicef) Ya ce Da Akwai Abin Damuwa Akan halin da kananan yaran gabacin Ukraine su ke ciki.

Asusun Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya ( Unicef) Ya ce Da Akwai Abin Damuwa Akan halin da kananan yaran gabacin Ukraine su ke ciki.

Kamfanin Dillancin Labarun Xinhua na kasar Sin, ya ambato asusun kare kananan yaran na majalisar dinkin duniya yana yin gargadi akan halin da kananan yaran garin Avdiivka da ke gabacin Ukraine su ke ciki, tare da cewa; Da akwai raya 17,000 da su ka kunshi wasu 500 da su ke rayuwa a cikin sanyin kankara, ba tare da abin dumama gidaje ko wutar lantarki  ba.

Kakakin Majalisar Dinkin Duniya, stephane dujarric yana cewa; Kawo ya zuwa yanzu an rufe makarantu 6 da kuma na kananan yara 4 saboda rikicin da yankin ya ke gani.

stephane dujarric ya kara da cewa; halin da ake ciki zai kawo koma baya a harkar karatu a yankin da kuma jefa kananan yara cikin damuwa.

Tun a 2014 ne da aka sami sauyin gwamnati mai ra'ayin yammacin turai  a Ukraine, kasar ta fada cikin rashin tsaro. 

Tags