Kwamitin Tsaron MDD Ya Fara Taro Kan Kasar Siriya
Kwamitin tsaron MDD ya fara gudanar da taro kan yanayin da Al'ummar kasar Siriya ke ciki a birnin New York na kasar Amurka.
A marecen yau Alkhamis ne Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fara gudanar da taro kan halin da Al'ummar kasar Siriya ke ciki a birnin New York na kasar Amurka.
Bayan irin kashin da kungiyoyin 'yan ta'adda ke sha a hanun Dakarun kasar Siriya,Amurka ta zargi Gwamnatin Siriya da kai harin makami mai guba kan fararen hula a yankin Khan Shaihun dake kalkashin ikon 'yan ta'adda, lamarin da ya sanya Amurkan ta kai harin makami mai lizzami a sansanin Jiragen saman yaki na kasar Siriya a ranar 7 ga watan Avrilun da ya gabata, saidai hakan ya sanya dakarun kasar Siriyan kara kaimi wajen fadada hare-haren su kan 'yan ta'addar ISIS a yankin Humus.
Harin makamai mai Lizzami na kasar Amurka na zuwa ne a yayin da magabatan Siriya ke kira da a gudanar da bincike kan wadanda suka yi amfani da makami masu guban kan fararen a yankuna daban daban dake kalkashin ikon 'yan ta'adda a kasar ta Siriya.