May 02, 2017 14:36 UTC
  • Komitin Shirin Sake Nazarin Yerjejeniyar NPT Ya Fara Zamansa Na Farko

Konitin da aka kafa don shirya taron sake nazarin yerjejeniyar NPT ta hana yaduwar makaman Nuklia ya fara zamansa na farko a birni Vienna na kasar Austria.

A shekara ta 2020 ake saran za'a gudanar da taron sake nazarin yerjejeniyar ta NPT, sannan wannan komitin zai gabatar da shirye shiryen da suka dace, da kuma batutuwan da za'a tattaun a taron.

An samar da yerjejeniyar NPT ne a shekara ta 1970 sannan an tsawaitata a shekara ta 1995 zuwa wani lokacin da ba'a ambata ba. 

A halin yanzu dai kasashen duniya 191 suka rattaba hannu kan dokar, daga ciki har tare da kasashen 5 maso makaman nuklia kuma masu kujerun din din din a MDD.

Kasashen Pakistan Inda da HKI basu sanya hannu kan wannan yerjejeniyar ba duk da cewa sun mallaka makaman Nklia sannan Korea ta Arewa ta fice daga yerjejeniyar a shekara 2003.

Tags