Putin Ya Ce Trump Bai Baiwa Lavrov Bayyanan Sirri Ba
(last modified Wed, 17 May 2017 18:50:30 GMT )
May 17, 2017 18:50 UTC
  • Putin Ya Ce Trump Bai Baiwa Lavrov Bayyanan Sirri Ba

Shugaban Kasar Rasha yayi watsi da zarkin cewa Shugaban kasar Amurka ya baiwa Ministan harakokin wajen Rasha Sergei Lavrov bayyanan Sirri

Kamfanin dillancin labaran Sputnik ya nakalto Viladimin Putin Shugaban kasar Rasha cikin wani taron manema labarai da ya gudanar a wannan laraba a garin Suu Kyi na cewa maganar da ake cewa Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya baiwa Ministan harakokin wajen kasar Sergei Lavrov bayanan sirri karya tsantsa.

Putin ya siffanta wannan maudu'i da kafafen yada labaran kasar Amurka suka watsa a matsayin haukan siyasa sannan kuma ya ce idan Majalisar kasar Amurka taga akwai maslaha kuma ta  amince, to kasar Rasha na iya gabatar mata da cikekken bayyanin da Shugaba Trump ya tattauna da Ministan Harakokin wajen na Rasha.

Putin ya kara da cewa duk da cewa kasar Rasha ba ta niyar shiga cikin harakokin cikin gidan Amurka, to amma masu watsa wannan jita-jita su san cewa wannan zarki da suke yiwa Shugaba Trump illa ce suke yiwa kasar ta Amurka

Kafafen yada labaran kasar Amurka sun habarta cewa a makun da ya gabata Shugaba Trump ya baiwa Ministan harakokin wajen kasar Rasha bayyanan sirri a kan kungiyar ta'addancin nan ta ISIS a yayin ganawar su.