MDD Za Ta Tura Dakarunta Zuwa Kasar Libiya.
Manzon musaman na MDD a kasar Libiya ya ce nan ba da jimawa ba majalisar za ta tura dakarunta zuwa kasar Libiya
Jaridar Mastamba ta kasar Italiya ta nakalto Ghassan Salamé manzon MDD na musaman kan kasar Libiya na cewa nan da 'yan kwanaki masu zuwa Majalisar Dinkin Duniya za ta tura tawagar tsaro da ta kumshi sojoji 250 domin kare ma'aikatan ta a kasar, da zarar an tura wanan tawaga, MDD ta fara gudanar da ayyukanta a kasar ta libiya.
Jami'in ya ci gaba da cewa ayyukan MDD a kasar Libiya daga shekarar 2014 ba za su yiyu ba, har ila yau ya ce ya zama wajibi a zartar da dukkanin shawarwarin da aka gabatar na warware sabanin dake akwai tsakanin bangarorin kasar bisa sanya idon MDD.
Tun bayan kifar da gwamnatin marigayyi kanar Mu'ammar kaddafi a shekarar 2011, kasar Libiyan ta fada cikin rikici, wanda hakan ya bawa kungiyoyin 'yan ta'adda na duniya damar kutsawa cikin kasar.