Kwamitin Tsaro Ya Bukaci Saudiyya Ta Kawo Karshen Killace Yemen
Kwamitin tsaro na Majalisar dinkin duniya a bukaci kawacen da Saudiyya ke jagoranta da ya kawo karshen killacewar da ya yi wa kasar Yemen dake fuskantar barazana yunwa irinta mafi muni a shekarun goma da suka gabata.
A zaman da kwmaitin ya yi na sirri, kasashe mambobinsa 15 sun nuna matukar damuwarsu kan halin da ayyukan jin kai ke ciki , tun bayan da Saudiyya ta bada umurnin rufe tashoshin ruwa, na kasa da kuma na sama a kasar ta Yemen.
Shugaban kwamitin tsaro na wannan karo jakadan Italiya Sebastiano Cardi, ya ce dole ne fa kawancen ya bar a kai kayan agaji a kasar, don kada a shiga wata matsala wacce ta wuce ta baya.
Don haka a cewarsa gwamnatin ta Riyad ta bada umurnin bude dukkan tashohin kasa da na ruwa da na sama a kasar ta Yemen.
A ranar Litinin data gabata ne Saudiyya ta bada umurnin rufe dukkan tashofin na Yemen, bayan da 'yan gwagwarmayar neman sauyi na Houtsis suka harba wani makamin linzami a kusa da birnin Riyad a matsayin maida martani kan hare-hare zalincin shekaru biyu da Saudiyya ke kaiwa kasar wanda ya haifar da mutuwar dubban mutane galibi yara da mata, da kuma jefa kasar cikin masifar yunwa da barkewar cutar kwalera.