Dec 06, 2017 06:33 UTC
  • Thailand: An Dauke Wani Mutum Da Aka Sama Da Laifin Kai Harin Bom, Zaman Kurkuku Na Tsawon Shekaru 27

A yau laraba kotun ta daure mutumin mai shekaru 27 saboda samun sa da laifin kai hari da bom a asibitin Phramongkutklao da ke birnin Bankok a 2014

Asibitin dai na soja ne da ake yi wa sojoji masu aiki da wadanda su ka yi ritaya aiki da basu magani.

Mutumin mai suna Watana Pumret tsohon ma'aikacin gwamnati ne. Bayan yanke masa hukunci, an gan shi yana kuka yana kuma yin bankwana da matarsa.

A tsarin shari'a na kasar Thailand ba fadin sunayen alkalan da suka yanke hukunci sai a wasu shari'oi masu hatsarin gaske.

A shekarun baya kasar ta Thailand ta yi fama da hare-haren ta'addanci daga kungiyoyi daban-daban.

Tags