Amnesty International Ta Soki Birtaniyya Saboda Sayarwa Saudiyya Jiragen Yaki
Kungiyar kare hakkokin bil'adaman nan ta kasa da kasa Amnesty International ta yi kakkausar suka ga matakin da kasar Birtaniyya ta dauka na sayar wa Saudiyya da wasu jiragen yaki inda ta ce hakan tamkar kara rurar wutar yakin da ke faruwa a kasar Yemen ne.
Yayin da take mayar da martani kan yarjejeniyar sayar da makaman da Birtaniyyan ta cimma da Saudiyya, kungiyar ta Amnesty International ta bakin babbar daraktanta na Birtaniyya Kate Allen ta bayyana cewar: "Sayar da wasu karin jiragen yaki ga kasar da take jagorantar yaki na hadin gwiwa da ya ke ci gaba da ruguza gidaje, asibitoci da makarantu a Yemen, kawai kara man fetur ne ga wutar yaki da kara sanya bil'adama cikin mawuyacin hali“.
A jiya ne dai Saudiyya da Birtaniyya suka sanya hannu kan wata yarjejeniya sayen makamai inda a cikinta Birtaniyyan za ta sayar wa Saudiyyan da jiragen yakin samfurin Eurofighter Typhoon guda 48 ba tare da sun yi karin bayani dangane da yawan kudinsu ba. An cimma yarjejeniyar ce dai a jiyar Juma'a a rana ta karshe ta ziyarar da Yarima mai jiran gado na Saudiyya Muhammad bn Salman ya kai Birtaniyyan.
Ziyarar da Bn Salman dai ta fuskanci zanga-zangogi da tofin Allah tsine daga bangarori daban-daban na al'ummar Birtaniyyan sakamakon jagorantar ci gaba da zubar da jinin al'ummar kasar Yemen da yake yi a ci gaba da yakin da Saudiyya take jagoranta a kan al'ummar ta Yemen tun daga shekara ta 2015.