An Bukaci Zartar Da Yarjejjeniyar Tsagaita Wuta A Siriya
(last modified Sat, 17 Mar 2018 06:25:32 GMT )
Mar 17, 2018 06:25 UTC
  • An Bukaci Zartar Da Yarjejjeniyar Tsagaita Wuta A Siriya

Kwamitin tsaron MDD ya bukaci a zartar da yarjejjeniyar tsagaita wuta cikin gaggauwa a kasar Siriya

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar Sin ya nakalto Karel van Oosterom jakadan kasar Netherlands da ya karbi jagorancin kwamitin a cikin wannan wata na Maris da muke ciki ya ce manbobin kwamitin tsaro suna bukatar a zartar da kudiri mai lamba 2254 da kuma 2401 cikin gaggawa.

Mista Oosterom ya kara da cewa duk wani matsin lamba da kuma kuntatawa  kan fararen hula a yankunan dake karkashin mamayar 'yan ta'adda a yankin Ghouta ta gabas ya sabawa kudiri mai lamba ta 2401 da aka samar a watan Favrayu.

A nasa bangare,Staffan de Mistura jakadan MDD na musaman a kasar Siriya ya bukaci samar da hanyar kawo karshen rikicin kasar Siriya ta hanyar siyasa, sannan ya ce bai kamata ba a yanke kauna a game da hakan.