May 15, 2018 05:49 UTC
  • Duniya Na Ci Gaba Da Yin Tir Da Zubar Da Jini A Gaza

A daidai lokacin da yahudawan mamaya na Israila da Amurka ke murnar maida ofishin jakadancin Amurkar a birnin Kudus, kasashen duniya na ci gaba da yin allawadai da abunda wasunsu suka danganta da kisan kiyashi a Gaza.

Shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas ya yi tir da matakin tare da ayyana zaman makokin kwanaki 3 na juyayin shahidan da sojojin da Isra'ilan suka kashe.

A lokacin da yake tir da abunda ya danganta da kisan kiyashi daga gwamnatin ta'adanci ta Isra'ila, shi kuwa shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan ya ce Amurka ta rasa kimarta ta mai shiga tsakani a rikicin da ke faruwa a yankin gabas ta tsakiya. 

Ita ma dai Siriya, ta yi allawadai da abunda ta danganta da kisan gilla kan Palasdinawa na yahudawan mamaya na Israila.

Jamhuriya Musulinci ta Iran, ta bakin ministan harkokin wajenta, Muhammad Jawwad Zarif, tir ta yi da zubar da jinin bayun Allah 'yan Palasdinu.

Kasar Kowait kuwa kiran taron gaggawa ta yi na kwamitin tsaron MDD a yau Talata.

 A bangaren kasashen Turai kuwa, Faransa ma allawadai ta yi da abunda ta ke amfani da karfi kan Palasdinawa dake zanga zanga lumana a yayin da da Biritaniya ta bukaci Israila ta yi sassauci a cikin lamarin ta daina amfani da harbin bindiga.

Tags