Jun 16, 2018 06:29 UTC
  • Switzerland Ta Bukaci Dage Dokar Hana Sayar Da Makamai Ga Kasashen Da Suke Cikin Yakin Basasa

Gwamnatin Switzerland ta gabatar da bukatar ganin an dage dokar hana sayar da makamai ga kasashen da suke fama da yakin basasa.

A bayanin da gwamnatin Switzerland ta fitar ta bukaci ganin an bada 'yanci ga duk wata kasa a duniya kan sayar makamai da na'urorin yakin da take bukata, kuma koda kasar tana fama da matsalar yakin basasa.

Bayanin ya kara da cewa: Babu dalilin cewa duk kasar da take fama da yakin basasa zata yi amfani da makamai da na'urorin da ta saya a fagen ruruta wutan yakin da ke faruwa a cikin kasarta. Kamar yadda wannan sabuwar mahanga ta gwamnatin Switzerland bata nufin amincewa da sayar da makamai ga irin kasashen Yamen, Siriya da sauransu da suke cikin masifar yakin basasa.

Har ila yau kakakin ma'aikatar kasuwanci ta kasar Switzerland Fabian Meinifish ya fayyace cewa: Wannan sabon mahanga ta gwamnatin Switzerland ba tana nufin za a gabatar da ita a matsayar daftarin doka da za a gudanar da zaben jin ra'ayin jama'a kanta.   

 

Tags