Feb 11, 2018 19:06 UTC
  • Jiragen Saman Yakin Saudiyya Suna Ci Gaba Da Kashe Fararen Hula A Kasar Yamen

Jiragen saman yakin masarautar Saudiyya sun yi luguden wuta kan yankuna daban daban na kasar Yamen, inda suka kashe fararen hula akalla 9, kuma 5 daga cikinsu mata.

Gidan talabijin na Al-Masira na kasar Yamen ya watsa rahoton cewa: Jiragen saman yakin masarautar Saudiyya sun kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan yankunan lardin Hudaidah da ke yammacin kasar Yamen, inda suka kashe mutane akalla 9, kuma 5 daga cikinsu mata.

kamar yadda jiragen saman yakin na Saudiyya suka yi luguden wuta kan yankunan lardin Sa'adah da ke arewacin kasar ta Yamen a yau Lahadi, inda hare-haren suka janyo hasarar rayuka da na dukiyoyin al'umma musamman rusa gidaje.

Haka nan jiragen saman yakin na Saudiyya sun yi luguden wuta kan sansanin sojojin Yamen da ke yankin Al-Dilami a lardin Sa'adah.

Tun a watan Maris na shekara ta 2015 ne masarautar Saudiyya ta fara kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yamen, inda bayan kasa cimma bakar aniyarta ta hada rundunar hadin gwiwa daga kawayenta na kasashen Larabawa tare da tallafin kasashen Amurka da Birtaniya da nufin murkushe al'ummar Yamen da suka ki mika wuya ga bakar siyasarta amma har yanzu hakarta ta kasa cimma ruwa.

Tags