Amurka Ta Tsawaita Takunkumanta Kan Labanon
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya tsawaita takunkuman da gwamnatinsa ta dorawa kasar Labanon kan abinda ya kira "barazanar tsaro ga yan kasar Amurka" na tsawon shekara guda.
Kamfanin dillancin labaran Farsnews na kasar Iran ya bayyana cewa a shekara ta 2007 na shugaban kasar Amurka na lokacin ya dorawa gwamnatin kasar Lebanon wadannan takunkumai don abinda ya kira na barazanar kungiyar Hizbullah na kasar ga tsaron kasar Iran.
Har'ila yau gwamnatin Amurka ta zargin kungiyar ta Hizbullah da hargitsa lamura a yankin gabas ta tsakiya. Gwamnatin Amurka ta kara tsawaita wannan takunkumin ne bayan da kungiyar huzbullah da kawayenta suka sami kujeru 67 daga cikin kujeru 128 a zaben majalisar dokokin kasar ta Labanon wanda aka gudanar a cikin watan Mayun da ya gabata.
Banda takunkuman dai gwamnatin kasar Amurka tana takurawa jami'an gwamnatin kasar ta Lebanon don su yi watsi da kungiyar hizbullah wacce a halin yanzu ta zama gantsigi a cikin ginshikan gwamnatin kasar ta Labanon.