Aug 09, 2018 06:57 UTC
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci Myanmar Ta Shiryawa Yan Gudun Hijirar Kasar Yankinsu Don Maidasu Gida.

Kungiyar bada agajin gaggawa ta majalisar dinkin duniya ta bukaci kasar Myanmar ta gyara yankin Rokhin na kasar don shirin maida dubban daruruwan yan kasar wadanda suke gudun hijira a kasar Bangladesh a halin yanzu.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya nakalto Babban Kwamishina a hukumar bada agaji ga yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya (UNDP) yana fadar haka a wani rahoton hadin guiwa da wasu kungiyar bada agaji da suka fitar aa jiya Laraba. 

Kwamishinan ya kara da cewa kungiyar bada agaji suna bukatar samun damar shiga yankin Rokhin na kasar Myanmar don tabbatar da shirin maida yan gudun hijirar kasar yankunansu, sannan ya ce suna jiran majalisar dinkin duniya ta samar da rundunar tabbatar da zaman lafiya wacce za'a girketa a garin Maungdaw don tabbatar da lafiyan yan gudun hijirar.

Majalisar dinkin duniya ta rattaba hannu tare da gwamnatin kasar Myanmar a ranar 14 ga watan Yunin da ya gabata na maida yan  gudun hijirar kasar yankinsu na Rokhing. A halin yanzu dai a kasar Bangladesh kadai akwai yan gudun hijira kimanu dubu 700.  

Tags