Aug 11, 2018 06:44 UTC
  • An Tabbatar Da Tsohuwar Shugaban Kasar Cilly A Matsayin Shugaban Hukumar Kare Hakkin Bil'adama Ta MDD

Babban zauren majalisar dinkin duniya ta amince da Michelle Bachelet tsohuwar shugaban kasar Chilly a matsayin sabon shugaban hukumar kare hakkin bil'adama ta majalisar dinkin duniya.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto babban sakataren majalisar dinkin duniya António Guterres yana godewa babban zauren majalisar bayan ta amince da Michelle Bachelet a matsayin wacce zata maye gurbin Zaid Ra'ad Al-Hussain wanda wa'adinsa a matsayin shugaban hukumar zai kare a cikin watan Augusta da muke ciki.

A ranar Laraba da ta gabata ce babban sakataren majalisar dinkin duniya ya zabi Michelle Bachelet a matsayin sabuwar shugaban hukumar kare hakkin bil'adama ta majalisar, wacce kuma babban zauren majalisar ta tabbatar a jiya jumma'a. 

Michelle Bachelet ta zama shugaban kasar Chilly macce ta farko daga shekara 2006- 2010 sannan aka sake zabenta a kan wannan kujerar daga shekara ta 2010-2013. Kafin mukaminta na yanzu dai Michelle Bachelet tana ira wakilya ce bangare kare hakkin mata a majalisar dinkin duniya.

Tags