Aug 14, 2018 19:29 UTC
  • Theresa May Ta Mayar da Martani Kan Harin Da Aka Kai Kusa Da Majalisar Birtaniya

Firayi ministar kasar Birtaniya Theresa May ta mayar da martani dangane da harin da aka kai yau a kusa da ginin majalisar dokokin Birtaniya da ke London, tare da bayyan shi mai girgiza zukata matuka.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya habarta cewa,a  lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai yau a birnin London, kakakin firayi ministar kasar Birtaniya ya bayyana cewa, harin ya saka Theresa May cikin kaduwa, inda ta bayyana cewa har yanzu Birtaniya na fuskantar barazanar ta'addanci da gaske.

A yau ne wani mutum dan shekaru 20 da haihuwa ya bi ta kan mutane a gefen majalisar dokokin kasar a cikin birnin London, inda hukumar 'yan sanda ta ce harin na ta'addanci ne.

Babu wanda ya rasa ransa sakamakon harin, amma mutane uku sun jikkata.

Tags