Aug 15, 2018 19:08 UTC
  • Jami'an Tsaro A Kasar Britania Sun Bayan Sunan Mutumin Da Ake Tuhuma Da Harin Ta'addanci Na Jiya

Jami'an tsaro a kasar Britania sun bayyana sunan mutumin da suka kama dangane da harin da aka kai kusa da majalisar dokokin kasar a jiya Talata a birnin London.

Tashar talabijin ta Rasha today ta nakalto wasu kafafen yada labarai na kasar Britani suna fadar cewa sunan mutumin shi ne Saleh Khadir dan shekara 29 a duniya kuma dan kasar ta Britania amma asalinsa dan kasar Sudan.

Labarin ya kara da cewa ba'a taba kama shi da wani laifi kafin jiya ba. Don haka sunansa baya cikin masu aikata laifuffuka a kasar ko a cikin kasashen turai. 

An kama Khadir a jiya Talata bayan ya tuka wata mota ya kuma burmata a kan wasu masu tafiya a gifen titi da kuma wani mahayin keke a kusa da majalisar dokokin kasar Britania ya ji masu rauni kafin ya burmata kan wani shinge a gefin titi kusa da wurin.

Majiyar jami'an tsaron ta kara da cewa shi kadai ne aka kama dangane da wannan batun sanna ana binciken wasu wurare uku , biyu Birmingham daya kuma a Nottingham dangane da harin..

 

Tags