Aug 20, 2018 18:13 UTC
  • Tsohon Ministan Kasar Jamus Ya Yi Suka Kan Bakar Siyasar Amurka Kan Kasar Turkiyya

Tsohon ministan harkokin wajen kasar Jamus ya yi kakkausar suka kan siyasar Amurka na kokarin wurga kasar Turkiyya cikin matsalar tattalin arziki.

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta kasar Jamus a bugunta na yau Litinin ta habarto cewa: Tsohon ministan harkokin wajen kasar ta Jamus Sigmar Hartmut Gabriel ya yi kira ga gwamnatin Jamus da sauran kasashen yammacin Turai da su nisanci bakar siyasar shugaban kasar Amurka Donald Trump kan kasar Turkiyya musamman bakar aniyarsa ta kokarin rusa harkar tattalin arzikin kasar.

Gabriel ya kara da cewa: Kasashen yammacin Turai su suka fi kusanci da kasar Turkiyya a kan kasar Amurka sakamakon haka duk wani matakin rusa harkar tattalin arzikin Turkiyya ko janyo rashin zaman lafiya a kasar lamari ne da zai cutar da su kafin Amurka musamman matakin da Turkiyya zata dauka na ficewa daga cikin kungiyar tsaro ta NATO da kuma matsalar kwararan 'yan gudun hijirar Turkiyya zuwa cikin kasashen yammacin Turai.  

 

Tags