Aug 23, 2018 18:59 UTC
  • Jam'iyyar Labo Ta Kasar Britania Ta Sauya Tunani Kan Ficewar Kasar Daga tarayyar Turai

A wani juyin ba zata jam'iyyar Labo ta kasar Britania ta bada sanarwan cewa a shirye take gudanar da wani zaben raba gardama dangane da ficewar kasar daga tarayyar Turai.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, a harin da ta hada shi da BBC sakataren shirin ficewa daga tarayyar Turai Sir Keir Starmer ya ce jam'iyyar tana son bawa majalisar dokokin kasar duk wani zabin da taga ya dace kan lamarin. 

A cikin watan Yunin shekara ta 2016 ne fiye da rabin mutanen Britania suka zabi ficewa daga kungiyar tarayyar Turai, wanda hakan ya tada wani rikicin siyasa da ya sa Priministan David Cameron ya aji mukaminsa, Sai dai wacce ta gaje shi Theresa May ta kasa cimma yerjejeniyar ficewa salim alim daga kungiyar. 

Shekara guda kenan da zaben raba gardamar, duk tare da barazanar ficewa daga kungiyar ba tare da yerjejeniyar ba,  daga Karshe Jam'iyyar Labo wacce ta jagoranci goyon bayan ficewar Britania daga kungiyar, ta mayarwa majalisar dokokin kasar nauyin yanke shawara ta karshen kan batun. 

 

Tags