Aug 25, 2018 12:04 UTC
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Kakkausar Suka Kan Halin Da 'Yan Rohingya ke Ciki

Majalisar dinkin duniya ta yi kakkausar suka dangane da irin mawuyacin halin da musulmi 'yan kabilar Rihingya suke ciki.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da kakakin babban sakataren majalisar dinkin duniya Stephane Dujarric ya yi, ya bayyana cewa, babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres na cikin damuwa matuka kan halin da muuslmi 'yan kabilar Rohingya suke ciki a Mayanmar.

Ya ce babban abin takaici ne irin halin da aka bar wadannan mutane a ciki, da kuma yadda aka yi musu cin zarafi da raba su da kaddarorinsu da kuma tilasta dubban daruruwa daga cikinsu yin hijira.

Ya ce babau wani hanzari da mahukuntan Myanmar za su bayar. Dole ne su dauki matakin kare rayukan wadannan mutane, kuma a tabbatar da an shirya mayar da wadanda suka yi gudun hijira zuwa yankunasu.

Tags