Sep 01, 2018 12:59 UTC
  • Rasha Ta Bayar Da Rahoto Kan Yunkurin Yin Amfani Da Makamai Masu Guba A Syria

Gwamnatin kasar Rasha ta mika wani rahoto ga majalisar dinkin duniya dangane da yunkurin da wasu kasashe suke yi na neman yin amfani da makamai masu guba a Syria, domin samun hujjar kai wa kasar harin soji.

Kamfanin dillancin labaran Sputnik ya bayar da rahoton cewa, ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Labrov ya sanar da cewa, a jiya Juma'a Rasha ta mika wa majalisar dinkin duniya rahoton da ta shirya kan yadda wasu kasashe tare da hadin baki da 'yan ta'adda suke hankoron yin mfani da makamai masu guba a kan faraen hula a yankin Idlib na Syria.

Ministan harkokin wajen na Rasha ya ce ya kamata majalaisar dinkin duniya ta sanya ido kan abin da yake faruwa a yankin Idlib na Syria, domin ana son a yi amfani da wadannan makmai ne domin a tuhumi gwamnatin Syria da aikata hakan, kamar yadda aka yi a lokutan baya, domin a samu hujjar kai mata hari.

Ya kara da cewa a mafi yawan lokuta ana shirya irin wanann wasan kwaikwayon na yin amfani da makamai masu guba a Syria ne a duk lokacin da sojojin Syria suke samun gagarumar nasara a kan 'yan ta'adda.

Tags